Yaƙi da jahilci Gwamnatin tarayya ta sha alwashin tallafa wa ‘yan Najeriya miliyan 50

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bai wa hukumar yaƙi da jahilci da bunƙasa ilimin manya ta ƙasa (NMEC) ta sha alwashin ilimantar da manya miliyan 50 ilimin zamani.

Ministan ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan zaman majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC).

Majalisar ta amince da cikakkken tsarin inshora a makarantu sakandaren gwamnati guda 180 da ake da su a Najeriya.

Ministan ya jaddada aniyar gwamnatin ta dakatar da kafa sabbin jami’o’i a Najeriya a shekarar da ta gabata na tsawon shekara 7, yana mai cewa ƙalubalen Najeriya ba na rashin makarantu ba ne.

A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, ya ce, ɗalibai 228,000 cikin miliyan 2.3 da suka rubuta jarrabawar shiga jami’a ta ƙasa (UTME) ne suka samu shiga jami’o’in gwamnati.

Game da cin gashin kan hukumar NMEC:

Mista Alausa ya ce, ‘yancin gashin kai da aka bai wa hukumar yaki da jahilci da ilimin manya ta ƙasa (NMEC) ya biyo bayan gabatar da jawabi da shugaban hukumar, farfesa Musa Maitafsir, ya yi kan shirinta na ilimantar da manya miliyan 50 nan da shekara 3.

“A yau, muna da ‘yan Najeriya kusan miliyan 56 waɗanda ba su iya karatu da rubutu ba,” Alausa ya faɗa. “Ba za mu lamunci ci gaba da zama da wannan adadi na marasa ilimi ba.”

Ya yi bayanin cewa hukumar za ta ƙarfafa shirye-shiryenta ne ta radiyo da talabijin da wayar da kan al’umma da kafa cibiyoyin koyar da ilimi a garuruwa.

An kafa hukumar NMEC da nufin yaƙi da jahilci da hanyoyin ilimantar da al’umma wanda ba sai sun shiga aji ba da ci gaba da neman ilimi da cusa ɗabi’ar neman ilimi domin cigaba mai ɗorewa na manyan mutane a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *