Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun kama wasu jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC na jabu a jihar bisa zargin fasa-kwaurin sace-sacen jama’a da kuma karbar kudade a hannun Jama’a.
Kamen ya biyo bayan wasu korafe-korafe da jama’a musamman matasa suka shigar, inda ake zargin jami’an EFCC na kutsawa gidajensu da daddare, suna kama su da karfin tsiya, su tafi da su tare da karbar makudan kudade a hannun su.
An tattaro cewa karuwar korafe-korafen wani bangare ne ya haifar da zanga-zangar “Kawo Karshen EFCC” a garin Ughelli wanda ya kai ga kona motoci sama da 13 tare da lalata kadarori a wasu lokutan baya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ga manema labarai a garin Warri a ranar Juma’a, inda ya ce “Rundunar ba ta yi na’am da korafe-korafen ba, saboda bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa masu aikata laifin ba jami’an EFCC ba ne kamar yadda ta ce, ana zarginsu ne.”
