Wani Sabon Hari Ya Ƙone Katuna Da Akwatunan Zaɓe A Ofishin INEC Na Ebonyi

Wani Sabon Hari Ya Ƙone Katuna Da Akwatunan Zaɓe A Ofishin INEC Na Ebonyi

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce an lalata wasu kayayyaki masu daraja da suka hada da akwatunan zabe, rumfunan zabe da na’urorin samar da wutar lantarki, bayan wani hari da aka kai ofishinta na karamar hukumar Izzi da ke Ebonyi.

Festus Okoye, Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zaɓe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce, Kwamishinan Zabe na INEC na jihar, REC, Onyeka Pauline Ugochi ya bada rahoton cewa wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin a safiyar jiya Lahadi.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe.

“Duk da cewa babu hasarar rayuka da aka samu a harin, babban gini da kuma sauran kayayyakin duk sun lalace.

“Wadannan sun hada da akwatunan zabe guda 340, rumfunan zabe 130, injinan wutar lantarki guda 14, manyan tankunan ajiyar ruwa, kayan ofis iri-iri da katunan zabe na dindindin (PVCs) da har yanzu ba a tantance yawansu ba” inji shi.

Okoye ya ce an ja hankalin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro kan lamarin kuma an fara bincike.

“Abin takaici, wannan shi ne hari na uku da aka kai ofishinmu na karamar hukumar cikin kasa da makonni uku bayan irin wannan harin da aka kai ofisoshinmu a Ogun da Osun a ranar 10 ga watan Nuwamba,” in ji Mista Okoye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *