Gwamnan Ondo Yace Dole Ne Yankin Kudu Ya Mulki Najeriya A 2023

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya dage cewa dole ne fadar shugaban Najeriya ta zo Kudu a 2023 don kada ta kawo cikas ga tsarin karɓa-karɓa a kasar.

Akeredolu ya ce mika mulki wata yarjejeniya ce da ba a rubuta ba a kasar tun bayan komawar mulkin farar hula a shekarar 1999, yana mai cewa dole ne a sauya tsarin yanzu.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba a taron tunawa da Farfesa Bankole Oke na tsangayar ilimin likitancin dabbobi na jami’ar Ibadan na tsawon shekara guda, a lokacin da yake gabatar da lacca.

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su tabbatar da cewa mulki bai dawo Arewa ba a karkashin abin da ya bayyana da sunan jam’iyyar da ta zabo dan kudu a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Ya ce, “Jam’iyyar da ta zabi wani daga Arewa a matsayin dan takararta na shugaban kasa ba ta yin hakan ne don amfanin kasa. (Peter) Obi yana da damar tsayawa takara domin shi dan Kudu ne.

“A shirye muke mu ba shi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa mulki ya dawo Kudu a 2023.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *