Masarautar Saudiyya ta sanar da cewa za ta dawo da adadin mahajjatan da ta ke baiwa Najeriya kafin barkewar cutar COVID-19. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Idan za a iya tunawa cewa an dakatar da aikin hajjin Makka da Madina ga matafiya na kasashen waje a 2020 da 2021 yayin da na 2022 aka rage adadin zuwa rabi.
Wannan ya sa Najeriya ta samu rabin (45,000) na adadin da aka ware mata a baya na 90,000.
Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar alhazai ta Najeriya Mousa Ubandawaki a wata sanarwa da ya fitar a ranar Larabar ya bayyana cewa babban darakta mai kula da alhazan Saudiyya a ma’aikatar aikin hajji da umrah bin Yusuf Alwani ne ya tabbatar musu da hakan
Bahauddeen yayin wani taron share fage na aikin hajjin 2023 ta hanyar bidiyo tare da Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zukrullah Kunle Hassan ya kara da cewa ka’idojin da ma’aikatar ta fitar na aikin Hajjin 2023 sun hada da cire ka’idojin gwajin cutar Corona wato PCR.
Ya kara da cewa za a kulla yarjejeniya kan masaukin mahajjata a ranar 10 ga Fabrairu, sauran kuma za a kammala su a ranar 24 ga Janairu shekara mai zuwa.
