Ahmed Lawan Ya Musanta Batun Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Na Machina

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada da ke nuni da cewa ya canja ra’ayinsa kan alkawarin da ya dauka na cewa ba zai daukaka kara kan hukuncin da kotu ta yanke kan dan takarar jam’iyyar APC na jihar Yobe ta Arewa ba a zaben 2023 ba.

Lawan, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, a ranar Asabar, ya bayyana rahoton da aka buga a wata jarida ta yanar gizo a matsayin “karya ce kawai”.

Shugaban Majalisar Dattawa mai wakiltar Yobe ta Arewa a Majalisar Dattawa a halin yanzu ya kara da cewa ba shi da niyyar daukaka kara a kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu a Jihar Yobe ta yanke a ranar Laraba 28 ga watan Satumba, 2022, wadda ta amince da Bashir Sheriff Machina a matsayin zababben dan takarar jam’iyyar APC na Yobe ta Arewa.

A cewar sanarwar, Lawan, ya lura cewa idan wani bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba kuma ya yanke hukuncin kalubalantarsa, to babu ruwansa da shi.

“Mun ga rahoton da Jaridar Sahara Reporters ta rawaito a yanar gizo dangane da dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 na Sanata a Yobe ta Arewa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *