Allah Ne Ya Zaɓi Atiku Ya Zama Shugaban Ƙasar Najeriya – Iyorchia Ayu
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya yi ikirarin cewa Allah ya zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban kasar Najeriya.
Ayu ya ce Allah ne ya zabi Atiku a matsayin shugaban Najeriya domin ya magance kalubalen da ke addabar Najeriya.
Da yake jawabi jiya a Bauchi yayin da yake karbar dubban masu sauya sheka, Ayu ya ce Allah ne ya zabi Atiku ya hada kan kasar nan.
Da yake lura da cewa Arewa maso Gabas ba ta taba samar da shugaban Najeriya ba, Ayu ya ce: “Amma a yau, Allah ya zabi Atiku Abubakar, wanda dan Arewa maso Gabas ne, domin ya gyara dukkan kalubalen da ke dagula al’ummar kasa da kuma hada kan ta.”
Ya kuma tabbatar wa da wadanda suka sauya sheka cewa za su ji dadin shigowa a cikin jam’iyyar PDP.
Ya kuma bayyana cewa masu kokarin kawo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar za su ji takaici.
“Akwai makiyan jam’iyyar da suka kuduri aniyar haifar da rarrabuwar kawuna a tsakaninmu ta hanyar yi mana karya iri-iri. Ina so in gaya muku cewa za su ji kunya domin a karshen ranar ’yan jam’iyyar za su fito gaba daya su kada kuri’a.
“Dukkan majalissar mu ta kasa, ‘yan takarar gwamna za su ci zaɓe. Da ya yi shekara takwas ba ta mulki, PDP za ta dawo mulki,” inji shi.
Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi ta kiraye-kirayen a tsige Ayu sakamakon fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ne ya jagoranci kiran a tsige Ayu.
Wike ya bayar da hujjar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da shugaban kasa ba za su iya fitowa daga yanki daya ba.
