A yau ne kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta yanke hukunci tsakanin Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, inda ta tabbatar wa da Gawuna nasara tare da yin watsi da bukatar Abba na kotun ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe ta yi a jihar Kano.
Bayan wannan hukunci Gawuna ya wallafa a Shafinsa ce yana gode ma Allah bisa wannan nasara da ya ba shi tare da rokon ya dafa ma ya samu ya fita kunyar mutanen Kano.
Ga dai abinda ya rubuta a shafin nasa na Facebook.
“Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Ba wayo ko dabarar mu bane mun yi imani nasarar mu daga Allah take, Ya Hayyu Ya Qayyum muna roƙon idan Ka tabbatar da mu Ka yi riƙo da hannayen mu, Ka sa mu fita kunyar Ka da kunyar al’ummar jihar Kano wajen yin abin da yake na dai-dai.”
