Al’ummar Jihar Zamfara Sun Koka Kan Tsananin Rayuwa A Dalilin Rashin Man Fetur
Mazauna jihar Zamfara sun koka kan yadda karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu ya durkusar da harkokin kasuwanci, ganin yadda ‘yan kasuwa da dama da ke dogaro da man fetur ba su iya biyan kudin siyan man fetur a wajan yan bunburutu.
Sun yi korafin cewa matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan ya zama abin kunya da rudani, inda suka ce gwamnatin tarayya da na jihohi sun kasa shawo kan munanan halin da ake ciki.
Wani mai sana’ar walda, Ibrahim Danbaba, ya bayyana lamarin a matsayin tsananin karancin man fetur, inda ya yi nuni da cewa wasu mutane ne ke haifar da rashin Man saboda son kai domin su yi arziki cikin dare daya.
Ya koka da cewa karancin man fetur na matukar shafar da harkokin kasuwanci, lamarin da ya sanya rayuwar al’umma cikin wahala.
Danbaba ya bayyana cewa, da zarar an samu karancin man fetur, ba ya shafar harkokin sufuri kadai, inda ya ke shafan komai gaba daya, yana mai jaddada cewa galibin mutane sun dogara ne da man fetur don rayuwarsu.
“Masu sayar da man fetur suna tara kayan man fetur a gidajen man da suke saida man ne kawai don sayar wa ‘yan kasuwar kan farashi mai tsada, ‘yan kasuwar su kuma suna sayar da man a farashin ninki biyu ga masu siye,” in ji shi.
Su ma masu tuka babura na kasuwanci sun koka da yadda harkokin kasuwanci ke tabarbarewa sakamakon karancin man fetur da ya addabi jihar, inda suka ce mutane da dama sun kasa biyan kudin aikinsu saboda tsadar.
