Amurka da Najeriya sun tattauna game da kare Kiristoci da yaki da ta’addanci

Amurka da Najeriya sun tattauna game da kare Kiristoci da yaki da ta’addanci

Amurka da Najeriya sun gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar hadin gwiwa, inda suka mayar da hankali kan kare al’ummomin Kirista a yankin Middle Belt da karfafa hukumomin shari’a da tsaro.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, taron ya gudana a Washington daga Laraba zuwa Alhamis, inda mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na Najeriya, Nuhu Ribadu, ya jagoranci tawagar Najeriya, yayin da Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Allison Hooker, ta jagoranci tawagar Amurka.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, bangarorin sun tattauna kan dawo da ’yan gudun hijira zuwa garuruwansu, gurfanar da wadanda ake zargi da ta’addanci, dakile hanyoyin samar da kudaden ta’addanci da kuma kara hadin gwiwar sojojin kasashen biyu.

Bangarorin sun kuma duba kalubalen da suka hada da asarar rayukan fararen hula da kuma gibin gaskiya wajen tafiyar da kudaden agajin jin kai.

Amurka ta yaba da kokarin Najeriya na gurfanar da daruruwan wadanda ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram da ISIS-West Africa, tare da kara karfin hukumomin shari’a da daukar karin ’yansanda 50,000.

Kasashen biyu sun amince cewa har yanzu akwai sauran aiki, musamman wajen tallafa wa ’yan gudun hijira da inganta hadin gwiwar yaki da ta’addanci da musayar bayanan sirri.

Taron na biyu ya biyo bayan na farko da aka gudanar a Abuja a watan Janairun 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *