An Bankaɗo Rijjyoyin Mai 58 Da Ake Satar Mai A Delta Da Bayelsa

An Bankaɗo Rijjyoyin Mai 58 Da Ake Satar Mai A Delta Da Bayelsa

Ya zuwa yanzu dai an gano haramtattun wuraren satar danyen man fetur guda 58 tun bayan fara aikin kawo karshen satar mai a magudanan ruwa na jihohin Delta da Bayelsa.

Tsohon shugaban tsagerun, Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Oporoza ranar Lahadin nan inda ya kuma yi karin haske kan gano bututun danyen mai mai tsawon kilomita 4 da ba bisa ka’ida ba a yankin Forcados na jihar Delta.

“Ina tsammanin mun gano sama da matatun mai 58 da aka samu a jihohin Delta da Bayelsa,” in ji shi.

A cewarsa, da wannan nasarar da aka samu, masu ruwa da tsaki a yankin na da kwarin gwiwar cewa za a samu nasara a yaki da satar danyen mai.

Tompolo ya kuma yabawa kokarin sojojin da kamfanin man fetur na Najeriya NNPC Limited bisa hadin kai da suka yi da shi kan aikin, inda ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don ganin an dakile wannan lamari.

“Ka sani, muna yin wannan aiki tare da jami’an tsaro. Muna ba da bayanan sirri ne kawai ga jami’an tsaro don taimakawa wajen yin aikin. Don haka, kowa da kowa – NNPC da sauran su – muna aiki tare cikin kyakkyawan yanayi a yanzu,” in ji Tompolo.

“Babbar matsalar ita ce rayuwar ruwa a yankin ta tafi. Muna yin duk abin da ya dace da ikonmu tare da sarakunan gargajiya da kowa da kowa don ganin cewa – tare da taimakon sojojin ruwa na Najeriya, hukumar DSS, da kowa da kowa – mun rage wannan zuwa mafi ƙanƙanta don mutanenmu su tsira bayan wannan lokaci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *