Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Babbar Hedikwatar tsaro ta Najeriya, tace rundunar ta ta “Operation Hadin Kai” ta halarka da Yan ta’adda 48 tare manyan shuwaganninsu guda shida, cikin makonni biyu a yakin Arewa Maso Gabacin Najeriya.
Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, Yan ta’addan 3,858 tare da iyalan nasu, Maza 505, Mata 1,042, sai kuma yara 2,311 ne suka janye kudurinsu a lokacin da kungiyar ke gudanar da Aiki.
Babban Daraktan tsaro, Major Janar Bernard Onyeuko ya bayyana hakan a ranar Alhamis din nan a Abuja, a lokacin da yake bayyana nasararorin da kungiyar ta samu a yayin gangamin yakar ta’addanci.
Ya Kara da cewa, sojojin sun yaki Yan Boko Haram da ISWAP.
Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan yuli sojin sama sun gudanar da Aiki a yankin Tumbum Jaki da Tumbum Murhu dake kusa da gabar tekun Chadi a jahar Borno inda sukayi nasarar Kashe Yan ta’adda sama da mutum 21.
Onyeuko ya bayyanar da cewa, manyan manyan shugabannin Yan ta’adda guda 6 sun ajiye makamansu ga sojojin A Gwoza.
Hakazalika hidikwatar tsaron ta lissafo sunayen shubannin Yan ta’addan kamar haka, Mala Hassan (wali), Ali Madagali (Munzur) Musa Bashir (Chief Anur), Buba Dahiru( Munzur), Jafar Hamma (Kaid), sai kuma Abbali Polisawa.
Mai magana da yawun Rundunar ya bayyana cewa, a lokacin yakin ,sojojin sun halarkar da mafi yawancin Yan ta’addan a wurare daban-daban a kauyen Gamage dake karamar hukumar Dikwa, da kuma Hanyar Dikwa zuwa Gamborou -Ngala, da hanya Pulka -Gwale dake a jahar Borno.
Ya Kara da cewa, Anyi nasarar kama da yawan masu samarwa Yan ta’addan makamai da masu taimkamasu tare da makamai daban-daban a wurare daban-daban a lokacin yakin.
” Daga cikinsu Akwai Mata biyu mai suna, Hauwa Gambo Da kuma Khadija Dirsa”.
