Yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ke jagorantar zaman majalisar zartarwa karo na 38, ba a hangi mataimakin gwamnan, Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda shi ne kwamishinan ilimi mai zurfi ba a yayin zaman.
An samu takun saka dai, tsakanin, Gwarzo da Gwamna Abba tun bayan sauya shekar Gwamnan zuwa APC inda mataimakin nasa ya ci gaba da zama a NNPP.
Ko a makon da ya gabata ma, majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamnan bisa zarginsa da karɓar toshiyar baki a lokacin da yake kwamishinan ƙananan hukumomi.
Sai dai a zaman majalisar na ranar Laraba, inda mataimakin Gwamnan ya saba halarta, ba ga fuskarsa a wajen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Haka kuma, Babu wata sanarwa a hukumance kan dalilan da yasa bai halarci zaman ba.
