ASUU Ta Caccaki Gbajabiamila, Tace Ya Yaudare Su Kan Janye Yajin Aiki

ASUU Ta Caccaki Gbajabiamila, Tace Ya Yaudare Su Kan Janye Yajin Aiki

Kungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta zargin kakkakin majalissar wakilai Femi Gbajabiamila, da yaudararta, bayan ya bukaci kungiyar ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni 8 ta na yi a watan Octoban shekarar nan, tare da yimata alkawarin cewa, ba tare da bata lokaci ba, gwamnatin tarayya za ta biya su dukkannin albashin su da suke bi.

Shugaban kungiyar, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana wannan matsayi ne a ranar Talata a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Tribune Online a lokacin da aka bukaci ya yi waiwaye game da tsoma bakin kakakin majalisar sannan kuma akasin haka kan halin da suke ciki da gwamnatin tarayya.

Ya ce ASUU na da sassauci ga shugaban majalisar kuma hakan ne ya sa kungiyar ta shiga tattaunawa da shi a matsayin maraba da shiga tsakani don warware matsalar da ke tsakaninta da gwamnatin tarayya.

Ya ce Gbajabiamila har ma ya gabatar da takarda da ya sanya wa hannu ga shugabannin ASUU da ke nuna muhimmancin gwamnati ta biya gaba daya albashin da mambobinta ke bin su na tsawon watanni takwas sannan kuma ta gaggauta daukar wasu matakai tare da bayyana yadda za a magance su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *