ASUU Ta Ce Ba Zata Iya Alƙawarin Cewa Ba Za Ta Tsunduma Yajin Aiki Ba A 2023
Tsohon shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa ba za a iya kawar da sabon yajin aikin malaman jami’o’in kasar nan ba a shekarar 2023.
Ogunyemi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake jawabi a Channels TV: cikin wani shiri mai suna “Retrospect, shiri na musamman na karshen Shekara.
Idan za a iya tunawa cewa ASUU ta fara yajin aiki ne wanda ya dauki sama da watanni takwas a shekarar 2022 biyo bayan bukatunta na inganta walwala da alawus alawus din mambobinta da sauransu.
Sai dai ASUU ta kawo karshen yajin aikin ne biyo bayan hukuncin da kotun masana’antu ta yanke na neman mambobinta da su koma bakin aiki.
Amma Gwamnatin Tarayya ta biya Malaman rabin albashin su na watan Oktoba ne kawai, bisa dalilinta na amfani da tsarin ba aiki ba albashi.
Ogunyemi ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta damu da halin da ASUU ke ciki ba, ya kuma bayyana cewa rashin adalci ne rashin biyan mambobinta bashin da suke bi.
