ASUU ta sake yi wa Gwamnatin Tarayya barazana kan albashi – Ta ce za ta ɗauki mataki nan da ƙarshen Maris

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (Academic Staff Union of Universities ASUU ta gargaɗi Gwamnatin Tarayya cewa za ta ɗauki mataki idan ba a cika biyan albashin malamai gaba ɗaya ba bisa yarjejeniyar 2025 kafin ƙarshen watan Maris. Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ya bayyana cewa malaman jami’a sun fara gajiya da jinkirin biyan haƙƙoƙinsu, yana mai jaddada cewa suna sa ran a biya dukkan albashi da alawus-alawus kamar yadda aka amince.

Piwuna ya ƙara da cewa duk da cewa an samu ɗan sauyi a albashin malamai tun daga watan Janairu, har yanzu ba a kammala aiwatar da yarjejeniyar ba, musamman ga wasu rukuni irin su malamai na wucin gadi (sabbatical da visiting). Ya ce har yanzu wasu daga cikinsu ba sa samun cikakken albashi saboda ƙarancin kuɗi a jami’o’in da suke aiki, sannan wasu muhimman alawus-alawus kamar Earned Academic Allowances (EAA) ba a biya su gaba ɗaya ba.

Shugaban ASUU ya kuma zargi jinkirin kasafin kuɗin ƙasa da karkata hankali zuwa siyasa kafin zaɓen 2027 a matsayin manyan dalilan matsalar. Ya bayyana cewa yarjejeniyar 2025 ta ƙunshi ƙarin kaso 40% a alawus, inganta albashi da walwala, da kuma wasu muhimman tsare-tsare kamar kafa cibiyar bincike ta ƙasa da asusun tallafin Naira biliyan 30. Sai dai ya nuna damuwa cewa gwamnati ba ta nuna ƙwazo wajen cika waɗannan alkawurra ba, yana mai gargadin cewa idan ba a cika su nan da ƙarshen Maris ba, ƙungiyar za ta ɗauki mataki bisa dokokinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *