Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta musanta rahotannin da ke cewa dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso zai Marawa Ɗan Takarar PDP, Atiku Abubakar baya a zaben 2023.
Sakataren yada labarai na NNPP na kasa, Agbo Major, ya ce rahoton karya ne.
A wata sanarwa da ya fitar, Manjo ya kuma yi watsi da ikirarin cewa jam’iyyar NNPP ba ta la’akari da duk wani kawance da PDP gabanin zaben shugaban kasa na 2023.
Ya ce jam’iyyar NNPP za ta yi tunanin shiga kawance da duk wata jam’iyyar siyasa da ke son yin aiki da ita domin lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Major ya sake nanata cewa Kwankwaso ba zai bar takarar shugaban kasa a 2023 ba.
A cewar Major: “Kwankwaso ya kuduri aniyar tafiya gaba daya saboda kishinsa na yiwa ‘yan Najeriya hidima.
