Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google da ya rufe shafin yan kungiyar Rajin kafa kasar Biafra wato IPOB na You Tube.
Ministan yada Labaru da Al’adu na Kasa, Lai Mohammed ne yayi kiran inda ya ce Kungiyar ta IPOB haramtattar kungiya a kasar.
Mohammed ya sanar da hakan ne a lokacin ya karbi bakuncin jami’an kafar sadarwar ta Google a ranar Alhamis din nan a Abuja.
Ya lissafo sunayen Shafukan wadanda suka hada da Biafra Digest TV, Umu Biafra TV, da kuma Asa Biafra TV.
Ministan ya bayyana cewa, ire iren wadannan shafukan suna amfani da yarensu da yafi zama game gari a yankin lokacin yada shirye-shiryen na su wanda kuma suna yin haka ne domin su kauda hankalin mahukunta daga tunanin ko suna aikata wani abu maras kyau bare har a kawo batun tantance abinda su ke sakawa.
