Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NIGCOMSAT

Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NIGCOMSAT

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Injiniya Tukur Funtua a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Sadarwa ta Tauraron Ɗan Adam ta Najeriya NIGCOMSAT, biyo bayan yin riyatar shugaban hukumar Dr Abimbola Alale.

Wannan na kunshe ne acikin wata sanarwa data fito daga mataimakin mai bawa ministan sadarwa shawara akan kafafen yada Labarai Uwa Suleiman wacce aka rarrabawa manema labarai a ranar Juma’a .

An dai haifi Injiniya Tukur Mohammed Lawal a ranar ashirin da biyu ga watan Nuwambar 1966 a karamar hukumar Funtua Katsina yankin Arewa maso Yamma ta Najeriya.

Kafin a nadashi Tukur dai ya kasance shine daraktan kula da harkokin lafiyar Al’umma da muhallinsu na kamfanin BUA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *