Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kuɗin Shekarar 2023 A Watan Oktoba

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Shugaban Majalissar Wakilai na Ƙasa Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa, ana saran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gabatar Kasafin Kuɗin Shekarar 2023 a gaban Majalisar a watan Oktoba.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a ranar laraba bayan da ya duba wasu zauren Majalisar Mai lamba 028 da kuma mai lamba 234.

An samar da dakunan a matsayin na wucin gadi a matsayin zauren Majalisar a saboda da cigaba da gyare-gyaren da akayiwa Majalissar.

“Ina saran za’a gabatar da Kasafin Kuɗin a makon farko na watan Octoba,”ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa.

Ɗan Majalisar ya ƙara dacewa za’a ƙaddamar da zauren Majalisar na wuccin gadi kafin ranar 20 ga watan Satumba, ranar da Majalisar zata dawo da zaman ta.

“Daga karshe zamuyi alfahari da samun zauren Majalisa da za’a iya hadashi da wanda ake dashi a faɗin Duniya,” ya fada.

Gbajabiamila ya bayyana cewa idan aka kammala gyaran watan Ogustan Shekarar 2023 zai zama amfani ga Majalisa ta Goma masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *