Hukumar zaben ƙasar Kenya ta sanar da William Ruto a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, da kashi 50.49 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
An gudanar da zaɓen ne a ranar Talatar da ta gabata wato 9 ga watan Agustan 2022, an sanar da sakamakon a ranar Litinin.
A yayin da yake jawabi bayan sanar da nasararsa, William Ruto ya ce “Yammaci ne mai matuƙar daɗi, cike da farin ciki.
Tazarar da ke tsakaninsa da abokin fafatawarsa Raila Odinga ba shi da yawa, inda shi Odingan ya samu kashi 50.4 na yawan uri’un.
An jinkirta sanar da sakamakon saboda zarge-zargen maguɗi da aka dinga yi wa ɓangaren Odinga.
Huɗu daga cikin mambobin hukumar zaɓen bakwai sun ƙi su amince da a fitar da sanarwar sakamakon, suna cewa an yi maguɗi.
