Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu Ta Sake Hana Belin Abba Kyari
A ranar Talata ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da sabon buƙatar belin DCP Abba Kyari yayi.
Mai shari’a Emeka Nwite, a hukuncin da ya yanke, ya ce Mista Kyari bai bayar da isassun dalilan da za a amince da buƙatar ba.
Alkalin ya ce Ɗan sandan da ake tsare da shi ya kasa kawo sabbin bayanai a sabuwar bukatarsa bayan an ki amincewa da bukatar belin da aka yi masa a baya.
Sakamakon haka Mista Nwite ya dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga Oktoba, 20 da 21 ga Oktoba domin ci gaba da shari’ar.
A ranar 20 ga watan Yuli ne mai shari’a ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan karar belin da Mista Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda suka shigar da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, kan laifin miyagun kwayoyi.
