Da Ɗumi-Ɗuminsa: CBN Zai Sauya Fasalin Kuɗin Najeriya Daga Disamba

Babban bankin ƙasa CBN ya bayyana shirinsa na sauya fasalin wasu daga cikin kudaden da yan kasa ke amfani da su a harkokin cinikayya.

Gwamnan Bankin Godwin Emefele ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai yau Laraba a Abuja.

Emefele ya ce kudaden da bankin ke fatan sakewa fasali sun haɗar da Naira 200, 500, 1,000.

Wannan yunkurin bankin na zuwa ne a daidai lokacin da darajar Naira ke kara faduwa, a kasuwar musayar kudi. Yayin da Dalar Amurka ke ci gaba da yawan Gwauron zabi.

Har kawo wannan lokaci dai babu karin haske kan zuwa wane lokaci wannan sauyi zai bayyana ga yan kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *