Da Ɗuminsa: ASUU Ta Shigar Da Ƙara Kan Hukuncin Komawa Makaranta

Da Ɗuminsa: ASUU Ta Shigar Da Ƙara Kan Hukuncin Komawa Makaranta

Kungiyar malaman jami’o’i ta sha alwashin daukaka kara kan umarnin kotun kula da da’ai Ma’aikata ta kasa, inda ta umurci malaman da su koma bakin aikin au cikin gaggawa.

Kungiyar ta ce ta fara hada lauyoyinta karkashin jagorancin fitaccen dan rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, babban lauyan Najeriya, domin shigar da kara.

Shugaban kungiyar na shiyyar Legas, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar ya bukaci mambobin kungiyar da su kwantar da hankalinsu tare da hada kai don kai wa ga fafutukar har zuwa karshe.

ASUU ta fara yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu domin amsa bukatunta da suka hada da amincewa da tsarin biyan albashi da kungiyar ta fi so ayi amfani da shi a maimakon IPPIS naa Gwamnatin Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *