Shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda na kasa (PSC), Musiliu Smith ya yi murabus daga mukaminsa.
Daily Trust ta ruwiato cewa, masu fada aji a hukumar sun bukaci Smith ya yi murabus kuma ya amince da wannan bukata
Wata majiya mai tushe a hukumar ta shaida cewa Smith, tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sanda, ana sa ran mika shi ga mai shari’a Clara Ogunbiyi mai murabu dake wakiltar bangaren shari’a a hukumar.
Kakakin hukumar Ikechukwu Ani shi ma ya tabbatar wa wakilin Majiyar Mu murabus din ta wayar tarho.
An samu sabani tsakanin hukumar da ofishin Sufeto-Janar na ‘yan sandan kasar nan, kan ko wace hukuma ce ke da hakkin gudanar da aikin daukar sabbin Jami’an yan sanda a fadin kasar nan.
