Dalilin Da Ya Sa Atiku Bai Halarci Taron Tataunawa Da Yan Takara Ba – Okowa

Dalilin Da Ya Sa Atiku Bai Halarci Taron Tataunawa Da Yan Takara Ba – Okowa

 

Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya bayyana dalilin da ya sa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar bai halarci taron da aka gudanar a ranar Lahadi ba.

Taron zauren tattaunawar wanda gidan talabijin na Arise tare da hadin gwiwar Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaban al’umma (CDD) ne suka shirya taron kuma ya samu halartar ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabi’u Kwankwaso; Jam’iyyar Labour, Peter Obi; da Peoples Redemption Party, Kola Abiola.

A lokacin da aka fara zaman taron zauren tattaunawr, jama’a sun yi mamaki da suka samu labarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba zai samu halartar taron ba. Wannan ci gaban ya haifar da martani mara kyau da saɓani yayin da wasu daga cikin taron suka fara yin ruɗu, duk da haka, batun ya ƙare bayan wasu mintuna.

A yayin da yake mayar da martani kan hayaniyar, Okowa ya bayyana cewa wadanda suka shirya shirin suna sane da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba zai halarci taron tattaunawar ba.

Ya ci gaba da cewa ‘Ko wani shugaban kasa ne ko mataimakinsa tikitin daya ne’.

Gwamnan Jihar Delta ya ce, “Ina goyon bayan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP. Ina da masaniyar cewa akwai hanyar sadarwa da shi amma yana wajen kasar. Mun samu izinin masu shirya wannan shiri domin na wakilce shi. Taron zaure ne kuma an ba da uzuri yadda ya kamata.

“Ina ganin ya kamata a magance matsalar tada hankali da ke faruwa. Idan lokacin muhawara ya yi, sai mu shiga muhawarar; amma a wannan karon, taron ne na zauren tattauawa game da sanar da jama’a. Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, hamshakin dan kasuwa ne kuma wanda yake gudanar da wata cibiya ta ilimi. Ya yi imani da kasar nan.

“Atiku Abubakar ya nemi na wakilce shi kuma muna da takarda; Alkawari na da Najeriya. Takarda ce ta gama-gari a madadin kansa da ni da kuma jam’iyyar PDP. Da farko dai batun da muke magana akai shi ne na kasa. Ina tsammanin kasuwanci ne mai tsanani.

“Ko wane shugaban kasa ne ko mataimakin shugaban kasa tikitin daya ne kuma dole ne mu lura da hakan. Dole ne kuma mu fahimci cewa ci gaba a wannan al’umma, shi ne shugabanci na gari.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *