Dalilin Ziyarar Shettima, Zulum Villa, Bayan Bayyana Shettima Abokin Takarar Tinubu
Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Tsohon Gwamnan Jahar Borno , Sanata Kashim Shettima a ranar Laraba ya ziyarci Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Villa dake Abuja, bayan bayyanar dashi a matsayin mataimakin Ɗan Takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
Abokin Takarar Ɗan takarar Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya Isa ofishin shugaban kasar da misalin ƙarfe 3:40pm Wanda ya samu rakiyar Gwamnan jahar Borno Babagana Zulum .
Har zuwa kammala wannan rahoton, ba’a samu Cikakken bayanan ganawa da Shugaba Buhari ba.
A ranar 10 ga watan yuli Tinubu ya bayyana cewa, bayan dukkanin binciken daya gabata ya zabi Shettima saboda zai iya gudanar da abubuwa domin jajircewar sa.
