Darakta janar na inuwar gwamnonin jam’iyyar APC, Salihu Lukman ya ajiye miƙaminsa.
Kamar yadda rahotanni suka nuna cewa ajiye miƙamin na sa na da alaƙa da rikincin da ke addabar jam’iyyar dangane da babban taron ta na ƙasa da zata yi.
An dai ruwaito cewa Lukman ya aje muƙamin ne a yayin da inuwar gwamnonin APC ɗin ke ganawa ta sirri a ranar lahadi da daddare inda suka ce ya faye surutu.
Sai dai wasu gwamnonin a wajen suka ganin cewa bai kamata a yi mashi maganar da zata har zuƙashi ba har ya aje muƙamin tunda dai yana magana ne a matsayinsa na Darakta janar ne.
