Dole Ku Sanya Ƙasar Nan Cikin Zukatan Ku – Shugaba Buhari Ga Ƴan Najeriya

Dole Ku Sanya Ƙasar Nan Cikin Zukatan Ku – Shugaba Buhari Ga Ƴan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su dau nauyin da ya rataya a wuyan kasar wajen inganta tattalin arziki da siyasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a Gusau ranar Asabar.

Buhari wanda Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Farfesa Isah Ali Pantami ya wakilta, ya ce kowanne dan kasa ne ke da alhakin kawo sauye-sauye a matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa na kasa.

Ko da yake shugabanni suna da rawar da za su taka fiye da sauran, kowane ɗan Najeriya yana buƙatar yin aiki daidai don samun ingantacciyar al’umma.

Shugaban ya kuma yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su rika nuna gaskiya, adalci da kuma kyautatawa a yayin da suke mu’amala da al’ummarsu, yayin da mabiya kuma su rika mutunta shugabanni da kuma kasancewa masu bin doka da oda.

Ya kara da cewa idan masu bin doka da oda suka mutunta doka za a samu Najeriya mafi inganci.

Daga nan sai ya yabawa Majalissar Sarkin Musulmi da Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato bisa gabatar da kuma ci gaba da gudanar da gasar karatun Al-Qur’ani a fadin tarayyar kasar nan tsawon shekaru 37.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *