Dole Sai Mun Canja Mummunan Salon Mulkin APC A 2023 – Atiku
Dan Takarar Shugaban kasa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sauya mugun halin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanya jama’a a dalilin salon mulkin ta.
Atiku ya yi wannan alkawari ne a garin Uyo na jihar Akwa Ibom a wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na 2023 na jam’iyyar PDP a ranar Litinin.
Wazirin Adamawa wanda ya jaddada kudirinsa na ceto Najeriya daga munanan shugabancin jam’iyyar APC ta shimfiɗa, ya tunatar da cewa a lokacin PDP ta yi mulki, kasar ta fi dacewa a dukkan bangarorin rayuwar kasa fiye da yadda ake samu a halin yanzu.
Ya ce, “Jam’iyyar APC ta gaza a kasar nan ta kowane fanni da suka hada da tsaro, tattalin arziki, da ilimi da sauransu.
“A lokacin da PDP ke mulki, ‘yan Najeriya sun san kwanciyar hankali a tattalin arzikinmu kuma batun rashin tsaro bai yi muni ba kamar yadda muke da shi a yau.
“Don haka ne muke yakin neman ceto kasar nan daga mummunan shugabancin da APC ta kai mu. Dole ne mu kubutar da Najeriya domin a fili yake cewa ba za mu iya sake baiwa jam’iyyar APC damar kara kai mu kan turbar da ta sanya ba.
“Dole ne mu dawo da jam’iyyar PDP a lokacin zabe domin PDP ce kadai jam’iyyar siyasa da ta tabbatar da gaskiya da kuma iya sauya mugun halin da APC ta gindaya.
“Aiki mafi mahimmanci a gaban shugaban kasar nan na gaba shi ne hada kan kasa kuma babu wani daga cikin ‘yan takara a wannan zabe da zai iya yin ikirarin yin hakan fiye da ni da kuma ka’idojin shigar da jam’iyyar PDP,” Atiku. yace.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya ce jam’iyyar za ta shiga wannan kamfen a matsayin kungiya daya.
