Duk Da Rikicin Dake Tsakanin, Wike Ya Shiga Cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Atiku

Duk da zargin da ake yi cewa Arewa ta dauki nauyin rike madafun iko a jam’iyyar PDP, jam’iyyar ta nada Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a matsayin babban Darakta na Kwamorin yakin neman zabe na Shugaban Kasa (PCO) a zaben 2023.

Yayin da Tambuwal ke matsayin babban Darakta na Kwamitin yakin neman zabe na Kasa (NCMC), Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom shi ne Shugaban yakin neman zaben Shugaban Kasa (PCC).

Sauran sun hada da Gwamna Bala Mohammed (Bauchi) Mataimakin Shugaban PCC na Arewa da Gwamna Seyi Makinde (Oyo), Mataimakin Shugaban Kudu.

Daga cikin mambobi 326 na kwamitin yakin neman zaben sun hada da Sanata Liyel Imoke, Mataimakin babban Darakta aiyuka, Farfesa Adewale Oladipo, Mataimakin babban Darakta na kwamitin, Cif Raymond Dokpehsi, Mataimakin babbar Darakta na Fasaha da Tsare-tsare da Cif Okwesilieze Nwodo, Mataimakin babban Darakta na Bincike da Dabaru.

Jerin sunayen ya kunshi sunayen tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, da kuma tsofaffin gwamnonin jam’iyyar, tsofaffin Ministoci da har yanzu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne, mambobin kwamitin amintattu na jam’iyyar.

Sanata David Mark, Bukola Saraki, Pius Ayim; Shi ma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekwerenmadu ya sanya sunayen.

Dukkanin Gwamnonin Jam’iyyar PDP su ma mambobin kwamitin ne ciki har da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da ke neman Shugaban Jam’iyyar Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Takardar da Daily Trust ta gani na dauke da sa hannun sakataren kwamitin na kasa Umar Mohammed Bature ya kuma kara da cewa za a kaddamar da mambobin ne a ranar 28 ga watan Satumba, 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *