Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsaki ya Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani Kan kiran da Gwamnoni suka yi ga shugaba Buhari da ya bada da ta bada umarni ga ma’aikata masu shekaru 50 dasu ajiye aiki .
Sabata Sani ya bayyana haka ne a ranar Lahadi na a shafinsa na Twitter ya inda ya ce, ya kamata Gwamnoni da ke fadar haka da su fara daga kansu tunda dukkansu suna sama da shekaru 50.
Shehu Sani dai ya kasance daga cikin mutanen da ke fadin ra’ayin bakinsu akan al’amuran da suka shafi Najeriya musamman ma ta fuskar kalubalantar wasu manufofi na gwamnati da ya ga yan kasa na fadin rashin gamsuwarsu a kai.
