Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa ta Najeriya, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), sun kama wasu mutane 15 da ake zargi da safarar wasu nau’in ma’adinai masu haɗari da ake dangantawa da “radioactive” a jihar Kaduna.
A cikin wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce jami’an sashen hukumar na shiyyar Kaduna ne suka kama mutanen, dukkansu maza, bisa zargin shiga harkar saye da sayar da ma’adinai masu haɗari ba bisa ka’ida ba.
Oyewale ya bayyana cewa kama mutanen ya biyo bayan bincike da sa ido da jami’an EFCC suka dade suna yi kan wasu da ake zargi da safarar ma’adinai masu guba ko masu hasken radiation (radioactive solid minerals) ba tare da izini ba.
