El-Rufa’i Ya Fusata Kan Matsalar Tsaro, Zai Maida Wasu Dazuzzuka Zuwa Madatsun Ruwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kammala shirye-shiryen gina madatsar ruwa a dazuzzukan da suka kai hekta 800,000 da ke tsakanin garuruwan Buruku da Birnin-Gwari, wanda a tsawon shekarun da suka gabata, sun kasance mafakar ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka.

Darakta-Janar na Hukumar Tsare-Tsare da Raya Birane ta Jihar Kaduna, Ismail Umaru-Dikko ne, ya bayyana haka a taron gabatar da zuba jari na Kaduna karo na 7 da ake gudanarwa.

A cewar shugaban KASUPDA, aikin dam din ba wai kawai zai magance matsalolin tsaro a jihar ba, har ma zai kawo karshen ambaliyar ruwa a cikin babban birnin Kaduna.

Ya ce, “Daga Buruku zuwa Birnin-Gwari da muke fama da fashi da makami tun a tarihi, ya koma wurin satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane da fashi.

“Don haka, muna jin cewa dole ne wani abu ya faru a can. Muna da kasa mai girman gaske wadda ba a taba amfani da ita a wurin ba, shi ya sa ba za mu iya nade hannayenmu kawai mu kyale masu laifi su ci gaba da cin gajiyar wannan kasa mai albarka ba.

“Saboda haka, mun fito da tsarin, muka gano cewa daga Buruku zuwa Birnin-Gwari, muna da fili kusan hekta 800,000 wanda kusan jihohi biyu ne a wani sashe na kasar nan. Muna ƙirƙirar dam a can.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *