Ganduje Na Nan Kan Bakanshi Na Sanya Hannu A Kan Hukuncin Kisa Da Kotu Ta Yanke Wa Abduljabbar
Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce yana nan kan maganarsa ta sanya hannu akan hukunci kotu da ta yanke wa Sheikh Abduljabbar Kabara hukuncin kisa bisa kama shi da laifin yin kalaman rashin ɗa’a ga Annabi Muhammad S A W.
Gwamnan na magana ne ta bakin kwamishinan shari’a na jahar, Lawan Musa a yayin da jaridar Aminya ta tuntuɓe shi kan hukuncin da kotun ta yi.
Lawan ya ce, matsayar ta Gwamna ba ta sauya ba yana nan a kan bakansa kamar yadda ya sanya hannun a kan hukuncin kisa ga mutanen da suka kashe Hanifa.
Ya ƙara da cewa akwai matakan da ya kamata a bi kafin nan da zaran an kawo ma Gwamnan zai sanya hannu a kai.
Ya ce babu wanda hukuma zata bari ya taka doka bugu da ƙari an ɗauki duk wani matakin da ya dace.
Hakazalika ya ce, an gurfanar da Abduljabbar ne a kotu domin bashi damar kare kanshi kuma kotu ta gamsu da dukanin hujjojin da suka bayar a kansa don haka ta yanke masa hukunci da ya dace da shi.
