Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya gargadi masu yada jita-jita da tada zaune tsaye cewa gwamnatinsa ba za ta bari a karya zaman lafiya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki ba. Ya ce duk wanda ya nemi tayar da fitina ko haddasa rikici ta hanyar yada karya, zai fuskanci hukunci bisa doka.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin shugabannin hukumomin tsaro domin buda baki a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim House, inda ya jaddada cewa siyasar Kaduna jiha ce mai sarkakiya da yalwar kabilu da addinai, don haka dole ne a kiyaye zaman lafiya da hadin kai.
Ya ce gwamnatinsa na maraba da suka daga bangaren adawa, amma ba za ta lamunci yada karya ko jita-jita domin haddasa rikici ba. A cewarsa, ‘yancin fadin albarkacin baki ba izini ba ne na yada labaran karya da za su jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
“Wasu suna zaune a gidajensu cikin walwala suna ta yada jita-jita ta kafafen sada zumunta. Kada a fake da ‘yancin magana domin tayar da fitina. Ba za mu amince da hakan ba a Jihar Kaduna,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma yi gargadin cewa za su dauki mataki kan duk masu kasuwancin rikici da ke kokarin tarwatsa zaman lafiyar da ake samu a yanzu da sunan siyasa, amma cikin iyakokin doka.
Ya kara da cewa Kaduna jiha ce da ta kunshi dukkan kabilu da addinai, kasancewar al’ummarta masu karbar baki ne da zaman tare, kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da kare wannan hadin kai.
Gwamna Uba Sani ya tunatar da shugabannin tsaro cewa nan ba da dadewa ba za a fara yakin neman zabe, ganin cewa zaben fidda gwani zai fara a watan Afrilu ya kare a watan Mayu, kamar yadda jadawalin da Hukumar INEC ta fitar ya nuna. Ya gargade su da su kasance cikin shiri, domin wasu ‘yan siyasa da suka fadi zabe kan nemi jawo rudani ta hanyar yada karya domin su nuna ana zaluntarsu.
Haka kuma ya bukaci karin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro, shugabannin kananan hukumomi da sarakuna da malaman addini a matakin kasa domin karfafa tattara bayanan sirri.
Gwamnan ya yaba da kokarin jami’an tsaro bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa, yana mai cewa tun bayan hawansa mulki, ba a samu rikicin kabilanci ko na addini ba a jihar. Duk da haka, ya ce ko da yake jihar na cikin kwanciyar hankali, kofarsa a bude take domin tattaunawa kan hanyoyin da za a kara inganta tsaro, musamman dangane da matsalolin ‘yan bindiga da satar mutane.
