Gwamnatin Gombe Za Ta Tsaida Albashin Malaman Jami’ar Jihar Idan Basu Koma Ba

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa ya yi kakkausan gargaɗi ga Malam ASUU na Jami’ar Jahar, yana mai cewa zai tsaida Albashin su idan har basu janye yajin aikin da suke yi ba.

Acewar sa tun daga lokacin da kungiyar ASUU, ta fara yajin-aiki ake biyan malaman jami’ar jihar gombe albashin su, ba tare da sun yi aiki ba.

Muhammadu Inuwa Yahaya yace, zai dakatar da albashin malaman jami’arsa idan suka ki dawowa aiki.

An gagara shawo kan ASUU a GSU A cewarsa, an yi kokarin tattaunawa da shugabannin jami’ar ta GSU da kuma reshen kungiyar ASUU na malaman jami’ar GSU, amma an gaza samun mafita.

Idan har malaman sun ki bude jami’ar domin a cigaba da karantar da yara kamar yadda aka bada umarni, gwamnatin jihar Gombe za ta daina biyan su albashi.

Gwamnan ya bayyana yadda yake biyan ma’aikatan jihar da ‘yan fansho albashinsu duk ranar 25 da 27 na kowane wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *