Gwamnatin PDP Zata Ƙirƙiro Da Ƴan Sandan Jihohi Domin Magance Matsalar Tsaron Najeriya – Okowa
Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa ya jaddada cewa Ƙirƙiro da ƴan sandan jihohi zai magance matsalar tsaron da Najeriya ke fuskan ta.
Okowa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a lokacin taron Ƙungiyar Ƙwararrun Akantoci ICAN da take shiryawa duk shekara shekara wanda ya gudana a Abuja a ranar Laraba.
Mataimakin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa mafi yawan yan Najeriya sun yarda da cewa kirkiro da ƴan sandan jiha zai rage yawan aikata ta’addanci a ƙasar nan.
Okowa ya bayyana rashin jindaɗi na yadda Gwamnatin Tarayya taƙi amincewa akan lamurran da Al’umma suka fi buƙata.
Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatin PDP zata baiwa Jihohi dama su dauki ƴan sandan su.
Kamfanin dillancin labarai ta naƙalto shi yana cewa Al’umma zasu tabbatar da tsaron rayuka da Dukiyoyin Al’umma.
