Gwamnatin Sokoto Ta Kashe Sama Da Biliyan 14 Wajen Biyan Kuɗin Tallafin Karatu Ga Ɗalibai

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 14 don bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar 46,000 daga shekarar 2016 zuwa 2022.

Gwamnan ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin na daga cikin mutane 77 da suka samu nasarar kammala karatun digiri na farko a manyan makarantun Indiya.

Mai Magana da yawun Tambuwal, Muhammad Bello, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, inda ya kara da cewa likitoci, injiniyoyi da lauyoyi sun fito daga cikinsu.

A cewar Bello, daya daga cikin daliban da suka yaye Hassan Usman daga kauyen Kofa da ke karamar hukumar Binji, ya zama wanda ya samu lambar azurfa ta farko a nahiyar Afirka, saboda kwazon da ya yi a fannin Bio-Medical Engineering.

Ya ce wani dalibi mai suna Muzammil Maidoki daga karamar hukumar Sakkwato ta Arewa, wanda kuma a lokacin da yake ci gaba da karatunsa ya haddace Alkur’ani mai girma da kuma Sahihul Bukhari, ya kammala karatun digiri na farko a fannin likitanci a jami’ar Nahda da ke kasar Sudan.

Ya ce Tambuwal, a lokacin da yake karbar daliban da suka yaye, ya umurci shugaban ma’aikata na jihar da ya tabbatar da cewa an dauki dukkan wadanda suka kammala karatun likitanci aiki ba tare da bata lokaci ba bayan sun kammala shirin yi wa matasa hidima.

Bello ya kara da cewa Tambuwal ya bayyana jin dadinsa da irin nasarorin da suka samu a fannin ilimi, inda ya baiwa wanda ya samu lambar azurfa kyauta domin ya yi digirinsa na biyu da kuma Digiri na uku.
Gwamnatin Sokoto Ta Kashewa Daliban Jihar Naira Biliyan 14

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *