Gwamnatin Tarayya ta ce ta damu da ayyukan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a kasar, ta kuma sake jaddada aniyar ta na gurfanar da mutanen da suka kasa bin dokokin kare muhalli.
Babban Darakta na Hukumar Kula da Muhalli ta Kasa (NESREA), Farfesa Aliyu Jauro ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan hukumar a ranar Alhamis din nan a Abuja.
Jauro ya ce NESREA na da alhakin aiwatar da duk dokokin muhalli, ka’idoji, manufofi, da da’a a kasar.
Ya ce hukumar ta kuma haramta matakai da amfani da kayan aiki ko fasahar da ke lalata ingancin muhalli.
Jauro ya ce a baya-bayan nan an cika hukumar da korafe-korafe da dama a kan yadda ayyukan masu aikin hakar ma’adanai ke kara tabarbarewa a kasar.
Ya ce lamarin ya haifar da fargabar gurbacewar muhalli da lalata filayen noma da gurbacewar ruwa musamman ma kogin Osun.
Shugaban NESREA ya ce irin wadannan ayyukan hakar ma’adanai ba sabon abu bane a yankin domin jihar tana kan wani tsari mai dimbin arzikin ma’adinai kamar zinari, tourmaline, tantalite da sauransu.
