Har Ɗan Kamfai Na Rinƙa Wanke Ma Wasu Matan Kannywood Lokacin Da Ina Yaron Ƴan Fim – Naburaska

Shahararren ɗan wasan hausa a masana’antar Kannywood Mustapha Naburaska ya bayyana ire-iren ayyukan da ya rinƙa yi ma waɗanda taurarinsu ke haskawa a wancan lokacin a kannywwod.

A cikin wani labari layi biyu da kafar sadarwar Alfijir radio ta wallafa, ta ruwaito cewa tauraro Naburaska ya ce ya rinka sawo sigari tare da yi ma ƴan fim wanki da guna wani lokacin har ɗan kamfai ya ke wanke ma wasu matan.

KARANTA KUMA:Abun Murna: Cikin Sati Ɗaya, Ƴan ISWAP 7,000 Sun miƙa Wuya — Inji Soji

Allah da iko sai gashi tauraron ya samu shahara kuma a yanzu haka Naburaska shene mai taimaka ma gwamna Ganduje shawara a kan farfaganda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *