Idan Dikko Raɗɗa Bai Yi Nasara Ba A Bangaren Tsaro Yan Katsina Ne Na Ba Su Yi Nasara Ba – Yankwani

Tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokoki ta jihar Katsina kuma jigo a Jam’iyyar NNPP, Sani Liti Yankwani ya ce jihar na bukatar gwamna jajirtaccen irin Dikko Raɗɗa.

Yankwani ya bayyana haka ne a yayin wata fira da manema labarai suka yi da shi game da matsalar tsaro a jihar Katsina da kuma yadda Gwamna Raɗɗa ya tunkare ta.

Ya ce hakika yana goyon bayan yadda Raɗɗa ya tukari matsalar musamman yadda ya ba matasa tirenin da makamai da ababen hawa domin tunkarar yan ta’addan da ke addabar jihar.

Yankwani ya ce hakika Dikko Raɗɗa ya nuna da gaske ya ke tunda har ikirari ya yi cewa yana iya bada ran shi don jihar Katsina ta samu zaman lafiya.

Ya kuma kalubalanci masu ganin kamar wannan shiri na gwamnan ba zai haifar da da mai ido ba.

Yana mai cewa duk ma su yin wannan fatan sun samu damar da zasu yi a baya amma ba su yi ba shine suke ganin ya za ai yaro kamar yadda suke ganin sa ya zo ya yi lokaci guda kuma abin ya samu nasara.

A karshe ya ce a halin da ake yanzu jihar na bukatar a ci gaba da addu’o’i da kuma ba gwamna goyon baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *