IG ya mika tsarin kafa ‘yansandan jihohi ga majalisar dattawa

Sufeto janar na ‘yansanda, Tunji Disu, ya mika wani cikakken tsari na kafa rundunar ‘yan sandan jihohi ga kwamitin majalisar dattawa da ke duba kundin tsarin mulkin 1999.

An mika takardar ne ta hannun Olu Ogunsakin, wanda ya wakilci IGP, inda ya gabatar da kundin mai shafi 75 dauke da shawarwari da tsare-tsare kan yadda za a kafa da tafiyar da ‘yan sandan jihohi.

Mai bai wa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce kwamitin ya karɓi rahoton ne a ranar Alhamis.

A cewar Ogunsakin, rahoton ya kunshi shawarwari na kwararru da aka tattara bayan tuntuba da nazari kan illolin shari’a, gudanarwa da tsaro da kafa ‘yan sandan jihohi zai haifar.

Da yake martani, Barau ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa ya dace da manufofin shugaban kasa Bola Tinubu na inganta tsaro a fadin kasar.

Ya kara da cewa kwamitin zai nazarci rahoton tare da sauran shawarwarin da aka gabatar domin gyaran kundin tsarin mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *