INEC Ta Fusata Kan Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Ta, Ta Yi Allah Wadai

INEC Ta Fusata Kan Harin Da Aka Kaiwa Ofishin Ta, Ta Yi Allah Wadai

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana rashin jindadinta akan harin da aka kaiwa babban Ofishinta na jihar Imo dake a garin Owerri.

Majiyar Jakadiya ta bada rahoton cewa wasu ƴan bindiga da ba’a san ko su wane ne ba, sun kai harin a ranar Litinin.

Wasu daka cikin gine ginen hukumar duk sun kama da wuta tare da kuma lalacewa bayan da aka dasa wa wurin bom.

Harin da da aka kai a Owerri an samu nasarar harbin mutane ukku daga cikin yan bindigar tare da shugabansu inda suka baƙunci lahira.

A cikin wata takarda da kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Ilmantar da masu kaɗa ƙuri’a Festus Okoye ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana lamarin a matsayin harin lalata kadarorin Hukumar.

Okoye ya kuma bayyana cewa Lamarin ya faru ne a ranar da za’a rarrabawa mutane wadanda sukayi rajista katunan zabensu domin babban zaben shekarar 2023.

Wannan shine hari na uku da aka kaiwa shelkwatar hukumar dake jihar Imo a yan makonni biyu tun biyo bayan harin farko da aka kai a karamar hukumar Orlu a ranar Alhamis daya ga watan Disambar da shekarar da muke ciki, da kuma harin da akai kai a karamar hukumar Oru ta yamma a ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *