INEC Ta Gargaɗi Jam’iyyu Da Ƴan Takara Kan Kalaman Ɓatanci – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa 18 da suka yi rijista da suka tsayar da ‘yan takara a zaben 2023 da su kaurace wa duk wani nau’in kalaman batanci ko kalaman nuna kiyayya da ka iya kawo cikas ga zaben.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargadin a ranar Litinin din nan a Legas a wajen taron karawa juna sani na kwana biyu da ake yi na karawa hukumar ci gaba, sabbin abubuwa, shirye-shiryen zaben 2023 da muhimman batutuwan da suka shafi dokar zabe ta 2022.

Gargadin na zuwa ne gabanin ranar Laraba da za a fara gudanar da yakin neman zabe na jam’iyyun.

Farfesa Yakubu wanda ya samu wakilcin kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar INEC, Festus Okoye, ya bukaci dukkan jam’iyyun da suka yi rajista da su yi nazari sosai tare da kula da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulki, Dokar Zabe, Dokar ‘Yan Sanda da Dokar Jama’a domin gudanar da yakin neman zabe da gangamin siyasa cikin kwanciyar hankali da lumana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *