INEC Ta Gargadi Masu Siyan Katin Zaɓe, Tace Ko Sun Siya Bazai Yi Masu Amfani Ba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ’yan siyasa da ke sayen katin zabe na dindindin (PVCs) don murde zaben 2023 na yin wani yunkuri ne na banza.

A cewar INEC, Na’urar BVAS, fasahar da za a yi amfani da ita wajen tantance masu kada kuri’a a shekarar 2023, za ta ki amsan bayanan mutanen da ba su keda asalin katin zaben na dindin ba wato PVC.

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, da suka hadar da kungiyar dattawan Arewa da kungiyar kare hakkin jama’a da tabbatar da mulki na gari, sun yi zargin cewa ‘yan siyasa na sayen katin zabe daga talakawan masu kada kuri’a domin yin magudi a zabe mai zuwa.

Sai dai Okoye a ranar Lahadin, ya bayyana siyan katin zaben amatsayin abun da “ba zai yi tasiri ba”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *