Jahilai Ne Kashi 30 Na Ƴan Najeriya – Inji Ministan Ilimi Adamu
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akalla kashi 30 na ‘yan Najeriya jahilai ne.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Legas, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Adamu ya yi jawabi ga kungiyar Marubuta littattfai ta Najeriya (EWAN) na shekarar 2022, taron koli mai taken ‘Zuwa Makarantun Don Tsaro a Najeriya’.
Vivian Wategre, Daraktan kula da ayyukan Ilimi a ma’aikatar ne ya wakilci ministan.
Ya kara da cewa ayyuka da manufofi game da makarantu masu aminci sun nuna himmar Gwamnatin Tarayya kan halin da Najeriya ke ciki a yanzu da kuma nan gaba.
Ministan ya ce kashi 31 cikin 100 na ‘yan kasar ba su iya rubutu da karatu ba a shekarar 2021, sabanin kashi 38 a shekarar 2015.
Adamu ya bayyana kudirin ma’aikatar wajen kara kaimi a fannin ilimin a kasar nan.
Ya ce kokarin da gwamnati ke yi na magance kalubalen ya hada da hada kai da jakadan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan fannin Ilimin Duniya.
