Jami’an Tsaro Sun Kubutar Da Mace 1 Daga Cikin Dalibai Mata 5 Na Jami’ar FUDMA Daga Hannun Yan Ta’adda

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta ce an samu nasarar kubutar da daliba daya daga cikin dalibai Mata biyar na jam’iyyar tarayya da ke Dutsinma a jihar FUDMA, da yan ta’adda suna yi garkuwa da su

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ASP Sadiq Abubakar ya tura a manhajar WhatsApp mallakin rundunar, ya ce an samu sa’ar kubutar da da dalibar daya daga cikin biyar a ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamban wannan shekarar ta 2023 a kauyen Bilbis da ke cikin jihar Zamfara.

Sai dai, ASP Sadiq ya ce rundunar ba za ta bayyana sunan dalibar ba saboda wasu dalilai na tsaro.

Ya kuma ce, rundunar hadin gwiwa da sauran rundunonin tsaro a jihar ta Katsina na iya kokarinsu don ganin an kubutar da sauran daliban hudu daga hannun yan ta’addan cikin koshin lafiya da aminci.

Ya kuma yaba wa dalibar dangane da irin bayanan da ta taimaka wa jami’an tsaro da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *