A daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya, masana da masu tsara manufofi za su hallara a Abuja domin tattauna yadda Afirka za ta tsara makomarta a cikin wannan sabon yanayi.
Ƙungiyar African Finance and Economics Association (AFEA) ta sanar da cewa babban taronta na shekara ta 2026 zai mayar da hankali kan “Shirin Ci gaban Geoeconomic na Afirka a Zamanin Sake Tsarin Duniya.” Taron, wanda Sashen Arts da Social Sciences na Nile University da ke Abuja zai karɓi bakunci daga 3 zuwa 5 ga Yuli, zai tattaro malamai, masu bincike, masu tsara manufofi da ɗaliban digiri na gaba domin nazarin yadda sauyin kawance da gasar manyan ƙasashe ke tasiri ga ci gaban Afirka.
Masu shirya taron sun buɗe ƙofa ga malamai su aiko da takardu da shawarwarin zaman tattaunawa, tare da bin ka’idojin gabatarwa da suka haɗa da taƙaitaccen bayani mai kalmomi 300 ko cikakken bincike. Kwamitin zaɓe zai tantance takardu bisa muhimmanci, ingancin bincike da dacewar jigo, yayin da za a wallafa waɗanda aka amince da su a kundin taron. Haka kuma, cikakkun takardun da suka iso kafin 2 ga Yuni, 2026 za su cancanci shiga gasar Kyautar Mafi Kyawun Takarda da kuma damar wallafawa cikin sauri a mujallar Journal of African Development.
