Ka Umarci Hukumomi Su Gyara Gadar Aaduin Data Ruguje – Ƴar Majalisa Ga Makinde

Hon. Olawumi Oladeji Ɗan Majalissar Dokokin Jihar Oyo ta buƙaci Gwamnan jihar Seyi Makinde da ya umarci Hukumar dake da alhakin gyara hanyoyi a Jihar data gyara Gadar data rushe.

Olajide ta bayyana hakan ne a ranar Talata.

Jaridar Daily POST ta bada rahoton cewa gadar Aaduin dake yankin Katangua na Ogbomoso ta rushe sakamakon mamakon ruwan sama Wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu bangarorin garin a makon da ya gabata.

Oladeji wace itace mai wakiltar Ogbomoso ta Arewa ta kuma bukaci Makinde da ya tattara dukkanin hukumomi dake da alhakin kula da gina hanyoyi dake jihar dasu gyara gadar data rushe.

Ƴar Majalisar jam’iyyar APC ta kuma yi kira ga Makinde daya umarci Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri dasu sanya kayan aiki a wurin domin kara gina gadar.

Ƴar a lokacin da take jawabi dangane da lamarin a zauren majalissar a ranar Talata ta bayyana cewa gadar ita kadai ce mahada data hada tsakanin Katangua da sauran yankunan Ogbomoso.

Ta kuma kara da cewa lalacewar gadar ta shafi tattalin arzikin Ogbomoso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *